Magunguna a musulunci


Magunguna A Musulunci



Daga cikin abubuwan da suka zama ruwan dare cikin Al’umma, zance kan Maganunnan Musulunci. Lalle Musulunci ya bada ta sa gudummawar kan harkar magani, Amma masu tallen Maganin gargajiya suna wuce gona da iri a kasar Hausa da sunan Musulunci. A Musulunce; kamar yadda Malamai sukace: Ana amincewa wani abu da ya zamanto magani ne a musulunce, idan ya cika wadannan sharruda: • In aka samu Qur’ani ko Hadisi sun ambaceshi a matsayin Magani. • Idan aka gwada a ka tabbatar da yana Maganin wannan cutar. • In aka samu shaidar Likitoci kan dacewarsa a matsayin Magani. • Ya zamanto baya kunshe da haramtaccen Sinadari. Kamar yadda Manzon Allah SAW bai yi magana kan dukkan cututtuka ba, domin jigon sakonsa Gyara alaka tsakanin bawa da Ubangiijnsa. Amma wannan ba ya na nufin cewa Manzon Allah bai ce komai ba. In ka bibiyi jinyar Manzon Allah za ka ga cewa: • Ya aikawa likitocin zamaninsa don su gwada masa maganin da ya dace da cutarsa. • Bai takaitu kan Addu’a ba. • Amma ya yiwa wassu likitocin gyara kan maganunnuwan da suka fada masa, kamar wanda ya ambaci kwado cikin maganinsa, sai Manzon Allah SAW yace: an hana kashe kwadi. Cikin Maganunnuwan da Manzon Allah SAW ya tabbatar suna maganin komai akwai:  ALHABBATUS SAWDA’U, Yace: “tana maganin komai in banda Mutuwa”  RUWAN ZAMZAM, yace: “Ruwan warkar da cuttutuka ne” In ka ga an yi amfani da su ba a sami biyan bukata ba, Matsala a ka samu kan yanda ya kamata a yi amfani da su. Likitoci musulmai aikinsu ne gudanar da bincike kan yadda ya kamata a yi amfani da su kan kowace cuta. Kamar yadda aka rawaito cewa Manzon Allah ya fadi maganunnuwan wasu daidayakun cututtuka.kamar su;  Ciwon kai  Ciwon ciki  Sarar Majizai da harbin Kunama  Zazzabi  Ciwon Baya.dss Abinda da ya kamata mu karkare zancen dashi, Fadin Manzon Allah SAW:“ Allah bai saukar da wata cuta ba, sai da ya saukar da maganinta tare da ita, wanda yasan hakan ya sani, wanda kuma ya jahilci hakan ya jahilta” Wannan kira ne da zaburarwa daga bakin Manzon Allah SAW kan maida hankali da dagewa wajen binciken maganunnuwa, amma kash! Sai muka zauna wassu kuma suka tashi. Amma don sunan wani dan itace yazo cikin Qur’ani ko Hadisi wannan bai isa ya maida shi magani da sunan musulunci ba, matukar ba a sami karin bayani daga bakin Manzon Allah ba. Kamar yadda ba abinda zai hana shi zama magani in har an gwada aka tabbatar yana warkarwa. Abin takaici ne kwarai yanda zaka ringa ganin masu tallen maganin gargajiya a kasuwanni da taron jama’a suna batsa suna talle da sunan Musulunci, kamar yadda magani daya kan cututtuka daban daban, tare da zugawa da koda kai kai kace su maroka ne su. A bangare guda kuma wassu duk da sunan Musulunci, Duk wani maganin da ke dauke da kalmar larabci shima maganin musulunci ne. kai Jama’a!!!! Wanna ya tuna min maganar Imamushafi’I yana kuka kan musulman zamaninsa sai yace: “ Sun yi sakaci da Ilimin likitanci, wanda shine daya bisa ukun Ilimi sun Kyale shi a hannun yahudu da Nasara” wannan zamaninsa fa kenan, yaya al’amarin ya ke yau a kasarmu? Allah yasa mu gane.

Comments

Popular posts from this blog

6 Health benefit of dates during iftar

Habbatus Sauda DA Amfaninta