Habbatus Sauda DA Amfaninta

Habbatus-Sauda/Habbal-Al-Barakah wata bishiya ce wacce ta ke kunshe da sinadarai masu albarka ga lafiyarmu da rayuwarmu. Habbatus-Sauda dadaddiyar bishiya ce wacce ta fi shahara a kasashen larabawa. In muka duba zamu ga cewa larabawa sun dade suna amfani da Habbatus-Sauda tare da kwayar irin sa wanda a ke yi wa lakabi da “ Irin Albarka”, don bayan magani da a ke yi da shi, larabawa na amfani da shi wajen kayata girkinsu.

A sunnance,  Manzo Allah (S.A.W) ya bayyana Habbatus-Sauda a matsayin waraka ce ga dukkan cututtuka. Maganin mutawa ne kadai Habbatus-Sauda ba ta yi.
Bukhari Bn Hajar (R.A): ya ce abin da ake nufi da Habbatus-Sauda shi ne magani ga dukkan cuta, sai dai tafi tasirintuwa idan aka hada ta da wani abun, misali zuma, man zaitun, da dai sauransu.
Kwayar irin Habbatus-Sauda da mansa ya dade ana amfani da shi. sama da shekaru aru-aru,  wajen magance matsalolin da suka shafi lafiyar jiki.
Kadan daga cikin lallurorin da irin kwayar Habbatus-Sauda da man Habbatus-sauda ke magancewa sune kamar haka:
*Ciwon Sikari ( Diabetes).
*Ciwon Daji ( Cancer).
*Ciwon Makogwaro.
*Ciwon kai mai tsanani.
* Ciwon Kunne
* Mura da Sanyi.
*Matsalolin Hanta.
*Mataslolin da suka shafi harshe, dadashi da hakori.
*Kawar da matsalolin fatar fuska.
*Kara karfin garkuwar jiki.
*Karin Mahaifa.
*Tsuro kan fata.
*Hawan jini.
*Amosarin gashin kai
*Shakuwa.
*Tsutsar ciki.
*Magance matsalolin mafitsara
*Kurajan fuska.*
*Kuturta.
*Zafin jiki.
*Ciwon kirji.
*Sanko ( baldness).
*Tari.
Gurbacewar  ciki.
*Zubewar   gashin kai.
*Hana Yaduwar kwayar cutar daji.
Yadda za ka amfani da man da irin kwaryar Habbatus-Sauda
1.CIWON SIKARI ( DAIBETES).
Ga masu fama da ciwon sikari, sai su samu zuma mai kyau su hada da man Habbatus- Sauda a mazubi mai tsafta, sai su gauraya wannan hadin. Za su sha cokali daya sau biyu a rana. Sannan yana da kyau su kauracewa shan sikari da duk wani nau’in kayan abincin da zai iya sa lallurar ta yi karfi.


Zuma
Zuma


2.CIWON DAJI (CANCER).
Ga mai fama da ciwon daji, sai ya samu man Habbatus-Sauda da zuma ya hada waje guda a mazubi mai tsafta, zai sha cokali daya kafin ya ci komai da safe, daya da rana, daya da daddare kafin ya  kwanta barci

3.HAWAN JINI.
Ga mai fama da hawan jini, a kullum za ka zuba rabin cokali na man Habbatus-Sauda a ruwan zafi daidai yadda za ka iya sha, bayan ya huce kanda, sai ka sha. Sannan ka kasance mai yawan amfani da tafarnuwa, a abinci, ko shayi. Motsa jiki musamman lokacin da rana ta fara fitowa kafin ta yi zafi sosai.


Tafarnuwa
Tafarnuwa

4.TARI.
Rabin cokali na man Habbatus-Sauda za ka zuba a cikin kofi daya na shayin kofi (Coffee)  za ka yi  haka sau biyu a rana, sannan ka shafa man Habbatus-Sauda a kirjin ka da kuma gadon bayanka.

5.KARIN MAHAIFA.
Abinda za ki yi anan shi ne, ki samu man Habbatus-Sauda da zuma ki hada waje daya. Yawan su ya zamo daya, sai ki zuba su a mazubi daya, za ki sha rabin cokali sau uku a rana.
6.CIWON KAI MAI TSANANI
Ga mai fama da matsalolin ciwon kai sai ya samu man Habbatus-Sauda ya shafa a gaba goshin sa, sannan ya dan diga kadan a hanci, bayan ga haka ya kasance mai cin irin habbatus-Sauda bayan an gasa shi kadan tare da zuma, akalla sau biyu  a kowace rana.
7.MURA DA SANYI
Ga mai fama da mura sai ya samu zuma ya hada da Man Habbatus-Sauda, sai ya sha rabin cokali  a kullum sannan ya diga man kadan a cikin hancinsa.
8.TSURO A KAN FATA.
Abinda za ka yi shi ne sai ka nika irin kwayar Habbatus- sauda , sai ka kwaba da ruwa, sannan ka shafa akan wannan tsiron. Sau biyu a rana.

9.MATSAlOLIN DA SUKA SHAFI HANCI DA MAKOGWARO.
Ga mai fama da irin wannan matsalolin, sai ya samu lemun tsami mai kyau, ya matse ruwan a kofi sannan  ya zuba ruwan zafi sosai akai, rabin  cokali na man habbatus- Sauda, sannan sai ya shaki wannan tiririn ruwan zafin. Haka zai yi sau biyu a rana


Lemon tsami
Lemon tsami

  1. INGANTA LAFIYAR FATA
Habbatus- Sauda za ki samu sai ki hada da man zaitun , sai ki wanke fuskar , wannan hadin za ki shafa a fuska , bayan awa daya sai ki wanke.
  1. ZUBEWAR GASHIN KAI.
Ga mata masu fama da matsalar zubewar gashi, sai su hada man Habbatus_Sauda da man Zaitun, bayan su tsefe gashin sai su bi layi-layi na gashin suna sa masa man tare da yiwa kan tausa. .
12.CIWON  KUNNE.
Irin kwayar Habbatus-Sauda za ka gasa shi sama-sama, sannan ka  ni ka shi , sai ka sa man Habbatus- sauda rabin cokali, man Zaitun rabin cokali, sai ka hadesu a mazubi mai kyau, sirinji zaka samu sai ka dure wannan hadin maganai aciki, zaka diga akunne sau biyu a rana,
  1. GURBACEWAR CIKI.
Ga mai  fama da, gurbacewa ciki , sai ya sa rabin cokali na man Habbatus-Sauda a cikin kofi daya kindirmo daya. Za ka sha sau biya a rana.


Kindirmo
Kindirmo

  1. INGANTA KARFIN GARKUWAR JIKI- Shan man Habbatus-Sauda na kara inganta karfin garkuwar dan Adam musamman in zai juri shan rabin cokali a kowace rana.
  2. CIWON BAYA.
Ga amasu fama matsalolin ciwon baya sai su , samu kamar cokali 1-2 na man Habbatus- Sauda sai ya dora akan wuta yayi dan dumi, wannan man zasu shafa a bayan su tare da yiwa wajen tausa , a hankali. Sannan su sha man Habbatus- Sauda, karamin cokali sau uku a rana.
  1. RAGE DAMUWA.
Ga masu fama da yawan damuwa , ko kuma su ji duk sun takura , sai su sa  rabin cokali na man Habbatus- Sauda  a shayi ko kuma a kofe ( coffee).


Kofin Kofi
Kofin Kofi

17.Matsalolin Al’ada.
Ga mace mai fama da matsalolin da suka shafi  al’ada sai ta samu zuma cokali  daya ta zuba a kofin ruwan dumi, sannan ta sa karami cokali na man Habbatus-Sauda, sai ki sha sau biyu a rana, har na tsawon kwana 40.
  1. Ciwon kirji.
Ga masu fama da ciwon kirji, sai ya samu, man Habbatus-Sauda ya  hada da zuma a waje daya, bayan su hada, sai su shafa a daidai inda yake ciwon tare da lailaya man sosai ta yadda zai ratsa cikin jikin sosai, sannan a sha cokali daya da safe da kuma yamma a kullum.
  1. TSUTSAR CIKI
Ga mai fama da tsutsar ciki, sai ya nika irin kwayar Habbatus-Sauda guda 14 ,  sai ya hada da rabin karamin cokali  na man Habbatus-Sauda tare da rabin- rabi karamin cokali na ruwan kal ( apple cider vinegar) sai a hada da ¼ litar ruwa. In shaa Allahu za’a samu sauki.
  1. SHAKUWA.
Aduk sanda ka ke fama da shakuwa sai ka tauna irin kwayar Man Habbatus- Sauda guda 7, kasha ½  cokali na Man Habbatus_Sauda tare da (butter) Man shanu.
  1. MAGANCE MATSALOLIN MAFITSARA.
Abinda za ka yi a duk sanda ka samu kanka a irin wannan yanayi sai ka,  samu ¼ na litar nono/kindurmo ka hada da ½ cokali na Man Habbatus-Sauda da cokali daya na zuma, sai ka hade su waje daya, zaka sha wannan akullum sau 2.

  1. HASKEN FATA.
Man Habbatus-Sauda na da amfani wajen haskaka fata, ba tare da ya haifar da wata illa ba. Abinda za ki yi, shi ne ki samu 50 grams na Man Habbatus-Sauda da 50 grams na Man Zaitun sai ki hada waje guda, za ki sha karamin cokali daya a kullum kafin cin abincin safe.
  1. KUTURTA( LEPROSY).
Ga mai fama da ciwon kuturta sai su matse lemun zaki a kofi daya sannan ya sa rabin cokali na man Habbatus-Sauda ya juya sosai, za ya sha sau biyu a rana. In shaa Allahu za’a samu waraka.
  1. AMOSARIN GASHIN KA.
Man Habbatus-Sauda 10 grams za ki hada da 30 grams na man Zaitu sannan ki zuba 30 grams na  lalle na gargajiya a ciki, kwabasu za kiyi sannan ki dan dumama shi akan wuta, bayan ya dan huce sai ki shafa wannan kwabin akan, sannan ki sa hular lede bayan minti 15-30 sai ki wanke, za ki iya yin haka sau biyu a sati.
25.ZAFIN JIKI.
Aduk sanda ka samu kanka a cikin yanayi na zafin jiki, sai ka zuba rabin cokali na man Habbatus-Sauda a cikin shayi mara madara, sai ka sha. Zaka iya cigaba dayi har sai zafin jikin  yayi sanyi.
26.KURAJAN FUSKA.
Ga masu fama da matsalolin kujane fuska sai ki samu abarba ki markadata sannan ki tace ruwan abarba a kofi, sai ki dauko man Habbatus-Sauda ki sa rabin cokali na man Habbatus-Sauda, in kuma baki da abarba sai kiyi amfani da lemun tsami mai manya-manya a maimakon abarba. Za ki sha kafin kici abinci da kuma da daddare kafin ki kwanta barci har na tsawon wata 1, sannan  za ki iya amfani (Kalonji pimple cream) na fuska. Yana da kyau ki daina cin abincin da zafi sosai.

Wandanna sune akdan daga cikin amfani ko tasirin Mai da kwayar irin Habbatus-Sauda ke samarwa ga lafiyar jikinmu. Amma abinda hankulan mu anan shi ne , in kazo siyan man Hbbatus-Sauda ko irin yana da kyau ka kula sosai , don wasu ana siyar masu da “ black caraway” amatsayin Man Habbatus-Sauda wanda kowanen su abu ne mabambanta.
Sannan yana da kyau ka kula da iya adadin da za kayi amfani da shi , domin amfanin da shi har yar zarta, ma’ana ya wuce misali na iya illatar da kai. Man Habbatus-Sauda, ana kiran sa da suna daban- daban, aduk inda ka ga an rubuta suna kamar haka “ Kalonji, Black cumin, Habal-al-baraka.” To shi ne black seed oil wato Habbatus-Sauda. Lafiyarka jarinka.

Comments

Popular posts from this blog

Magunguna a musulunci

Magungunan goma sha takwas (18) da zogale keyi ga jikin dan adam