Posts

Showing posts from April, 2018

Habbatus Sauda DA Amfaninta

Image
Habbatus-Sauda/Habbal-Al-Barak ah wata bishiya ce wacce ta ke kunshe da sinadarai masu albarka ga lafiyarmu da rayuwarmu. Habbatus-Sauda dadaddiyar bishiya ce wacce ta fi shahara a kasashen larabawa. In muka duba zamu ga cewa larabawa sun dade suna amfani da Habbatus-Sauda tare da kwayar irin sa wanda a ke yi wa lakabi da “ Irin Albarka”, don bayan magani da a ke yi da shi, larabawa na amfani da shi wajen kayata girkinsu. A sunnance,  Manzo Allah (S.A.W) ya bayyana Habbatus-Sauda a matsayin waraka ce ga dukkan cututtuka. Maganin mutawa ne kadai Habbatus-Sauda ba ta yi. Bukhari Bn Hajar (R.A): ya ce abin da ake nufi da Habbatus-Sauda shi ne magani ga dukkan cuta, sai dai tafi tasirintuwa idan aka hada ta da wani abun, misali zuma, man zaitun, da dai sauransu. Kwayar irin Habbatus-Sauda da mansa ya dade ana amfani da shi. sama da shekaru aru-aru,  wajen magance matsalolin da suka shafi lafiyar jiki. Kadan daga cikin lallurorin da irin kwayar Habbatus-Sauda da man Habbatus-sauda